1010 B
1010 B
Musa
Gaskiya
Musa annabi ne kuma shugaban mutanen Isra'ila tsawon shekaru sama da 40.
- Da Musa yake ɗan jariri, iyayen Musa suka sa shi a cikin kwando a ciyayin iwa na Kogin Nilu domin su ɓoye shi daga fir'auna a Masar. 'Yar'uwar Musa Maryamu ita ce ta lura da shi a wurin. Ran Musa ya tsira sa'ad da ɗiyar Fir'auna ta same shi ta ɗauke shi ta kai shi fada domin ta girmar da shi a matsayin ɗanta.
- Allah ya zaɓi Musa domin ya fitar da Isra'ilawa daga bauta a Masar ya kuma bishe su zuwa Ƙasar Alƙawari.
- Bayan da Isra'ilawa suka kubce daga Masar da lokacin da suke yawo a jeji, Allah ya ba Musa duwatsu biyu da Dokoki Goma a rubuce a kansu.
- Wajen ƙarshen rayuwarsa Musa ya hangi Kasar Alƙawari, amma bai shiga ya zauna a cikinta ba domin ya yiwa Allah rashin biyayya.
(Hakanan duba: Miriyam, Ƙasar Alƙawari, Dokoki Goma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 07:04
- Ayyukan Manzanni 07:30
- Fitowa 02:10
- Fitowa 09:01
- Matiyu 17:04
- Romawa 05:14