737 B
737 B
Mahallici
Gaskiya
A taƙaice "Mahallici" wani ne da yake hallita ko ya yi abubuwa.
- A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "Mahallici" ana amfani da ita a kira Yahweh, domin shi ne ya hallici komai da komai.
- Yawancin lokaci a kan haɗa da waɗannan kalmomi "na sa" ko "na wa" ko "na ku."
Shawarwarin Fassara:
- Wannan kalma "Mahallici" za a iya fassara ta haka "Mai Hallita" ko "Allah dake yin hallita" ko "Wanda ya yi komai da komai."
- Wannan furci "mahallicinsa" za a iya fassara ta haka "Wannan da ya hallice shi" ko "Allah daya hallice shi."
- Wannan furci "Mahallicin ka" da Mahallici na" za a iya basu fassara guda.
(Hakanan duba: hallici, Yahweh)
Wurarenda ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Hosiya 08:13-14