804 B
804 B
Yezriyel, Bayezriye
Gaskiya
Yezriyel wani birni ne mai muhimmanci a Isra'ila na kabilar Issaka, yana kudu maso yamma da Tekun Gishiri.
- Birnin Yezriyel yana ɗaya daga cikin mahaɗar yamma na Sararin Megiddo, wanda kuma ake kira "Kwarin Yezriyel."
- Sarakunan Isra'ila da yawa sunyi fãda-fãdarsu a cikin birnin Yezriyel.
- Garkar inabin Nabot na kusa da fãdar Sarki Ahab a cikin Yezriyel. Annabi Iliya yayi anabci gãba da Ahab a wurin.
- An kashe Yezebel muguwar matar Ahab a Yezriyel.
- Muhimman al'amura da yawa sun faru a wannan birni, harda yaƙe-yaƙe da yawa.
(Hakanan duba: Ahab, Iliya, Issaka, Yezebel, fãda, Tekun Gishiri)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sarakuna 04:12
- 1 Sama'ila 25:43-44
- 2 Sarakuna 08:28-29
- 2 Sama'ila 02:1-3
- Littafin Alƙalai 06:33