1.0 KiB
1.0 KiB
Yehoram, Yoram
Gaskiya
"Yehoram" suna ne na sarakuna biyu a Tsohon Alƙawari. Dukka sarakuna biyun kuma an sansu da suna "Yoram."
- Ɗaya Sarki Yehoram ɗin yayi mulki a masarautar Yahuda tsawon shekaru takwas. Shi ɗa ne ga Yehoshafat. Wannan sarkin ne aka fi sani da suna Yehoram.
- Ɗayan Sarki Yehoram ɗin yayi mulki a masarautar Isra'ila tsawon shekaru sha biyu. Shi ɗa ne ga Sarki Ahab.
- Sarki Yehoram na Yahuda yayi mulki a zamanin da annabawa Irmiya, Daniyel, Obadiya, da Ezekiyel suke annabci a masarautar Yahuda.
- Sarki Yehoram kuma yayi mulki wasu lokutta sa'ad da Yehoshafat mahaifinsa yake mulki a bisa Yahuda.
- A wasu juyin koyaushe suna amfani da sunan "Yehoram" sa'ad da ake ambaton wannan sarki na Isra'ila sa'an nan sunan "Yoram" domin sarkin Yahuda.
- Wata hanyar ta bambanta kowanne a sarari shine wurin haɗawa da sunan mahaifinsa.
(Hakanan duba: Ahab, Yehoshafat, Yoram, Yahuda, masarautar Isra'ila, Obadiya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sarakuna 22:48-50
- 2 Tarihi 21:03
- 2 Sarakuna 11:1-3
- 2 Sarakuna 12:18