691 B
691 B
Bahibite, Hibitiyawa
Gaskiya
Hibitiyawa su ne ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin mutane da ke zama a ƙasar Kan'ana.
- Dukkan waɗannan ƙungiyoyin, sun haɗa da Hibitiyawa, sun kasance ne daga Kan'ana, wanda ya kasance jikan Nuhu.
- Shekem Bahibite ya yiwa Dina 'yar yakubu fyɗe, ɗan'uwanta kuma ya kashe Hibitiyawa da yawa a matsayin ramako.
- Lokacin da Yoshuwa ya jagoranci Isra'ilawa su mallaki ƙasar Kan'ana, Isra'ilawa sun yi kasadar ƙulla ƙawance da Hibitiyawa a memakon mamaye su.
(Hakanan duba: Kan'ana, Hamor, Nuhu, Shekem)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Tarihi 08:7-8
- Fitowa 03:7-8
- Farawa 34:2
- Yoshuwa 09:1-2
- Littafin Alƙalai 03:1-3