956 B
956 B
Hananiya
Gaskiya
Hananiya suna ne na mutane mabambanta da yawa a cikin Tsohon Alƙawari.
- Ɗaya Hananiyan Ba'isra'ile ne da a ka kame zuwa bauta a Babila wanda a ka canjawa suna "Shadrak."
- An ba shi matsayi a matsayin mai hidima a gidan sarauta sabo da ƙwarewarsa da kuma halinsa mai martaba.
- A lokacin da a ka jefa Hananiya (Shadrak) da sauran abokansa biyu a cikin tanderun wuta sabo da sun ƙi bautawa sarkin Babila. Allah ya nuna ikonsa ta wurin kare su daga wutar.
- Wani mutum kuma mai suna Hananiya an lissafa shi a cikin zuriyar Sarkin Suleman.
- Wani Hananniya na da bam shi ne wani annabin ƙarya a kwanakin annabi Irmiya.
- Wani mutum kuma mai suna Hananiya firist ne wanda ya jagoranci gangamin murna a kwanakin Nehemiya.
(Hakanan duba: Azariya, Babila, Daniyel, annabin ƙarya, Irmiya, Mishayel)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Daniyel 01:6-7
- Daniyel 02:17-18
- Irmiya 28:1
- Irmiya 28:5-7
- Irmiya 28:15:17