756 B
756 B
Bashan
Gaskiya
Bashan wani yankin ƙasa ne gabas da Tekun Galili. Shi ne mamaye wajen da yau ake ce da shi Siriya da kuma Tuddan Golan.
- A Tsohon Alƙawari birnin mafaka da ake ce da shi "Golan" a wannan yankin Bashan yake.
- Bashan ƙasa ce mai armashi sananniya domin itatuwan riminta da makiyayar dabbobi.
- A Farawa 14 an rubuta cewa Bashan wurin yaƙi ne tsakanin sarakuna da yawa da al'ummarsu.
- A lokacin da Isra'ilawa suke yawo a jeji bayan fitowarsu daga Masar, sun ƙwace wani ɓangaren yankin Bashan.
- Bayan shekaru da dama, Suleman ya samo kayayyaki daga wannan yanki.
(Hakanan duba: Masar, rimi, Tekun Galili, Siriya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sarakuna 04:13
- Amos 04:01
- Irmiya 22:20-21
- Yoshuwa 09:10