710 B
710 B
Ba'asha
Gaskiya
Ba'asha ɗaya daga cikin mugayen sarakunan Isra'ila ne, wanda ya tunzura Isra'ilawa su yi sujada ga alloli.
- Ba'asha shi ne sarki na uku na Isra'ila kuma ya yi sarauta shekara ashirin da huɗu, lokacin da Asa ke sarauta a Yahuda.
- Shi hafsan sojoji ne wanda ya zama sarki ta wurin kashe sarki Nadab dake kan gadon sarauta a lokacin.
- A lokacin sarautar Ba'asha an yi yaƙe-yaƙe da yawa tsakanin mulkin Isra'ila dana Yahuda, musamman da Sarki Asa na Yahuda.
- Sabili da zunuban Ba'asha masu yawa Allah ya cire shi daga sarauta ta wurin mutuwarsa.
(Hakanan duba: Asa, allahn ƙarya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sarakuna 15:17
- 2 Sarakuna 09:09
- Irmiya 41:09