601 B
601 B
Ai
Gaskiya
A lokatanTsohon Alƙawari, Ai sunan wani garin Kan'aniyawa ne kudu da Betel ratan kilo mita 8 arewa maso yamma da Yeriko.
- Bayan ya ci Yeriko, Yoshuwa ya bida Isra'ilawa a kai harin ga Ai. Amma nan da nan aka buga su domin Allah bai ji daɗinsu ba.
- Wani Ba'isra'ile mai suna Akan ya saci ganima daga Yeriko sai Allah ya umarta a kashe shi da iyalinsa. Sa'annan ne Allah ya taimaki Isra'ilawa suka ci mutanen Ai da yaƙi.
(Hakanan duba: Betel, Yeriko)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ezra 02:27-30
- Farawa 12:8-9
- Farawa 13:3-4
- Yoshuwa 07:03
- Yoshuwa 08:12