883 B
883 B
Absalom
Gaskiya
Absalom ɗan Sarki Dauda na uku ne. Shi sananne ne domin kyaun jamalinsa da kuma zafin rai.
- Sa'ad da aka yi wa ƙanwar Absalom Tama fyaɗe ta wurin ɗan'uwansu, Amnon, wanda suke uba ɗaya, Absalom ya shirya ya sa a kashe Amnon.
- Bayan an kashe Amnon, Absalom ya gudu zuwa gundumar Geshu (inda mahaifiyarsa Ma'aka ta fito) ya kuma zauna a can har shekara uku. Sa'an nan Sarki Dauda ya aika ya komo zuwa Yerusalem, amma bai bari Absalom ya shigo gabansa ba har shekara biyu.
- Absalom ya juyar da waɗansu mutane gãba da Sarki Dauda ya bida tawaye gãba da shi.
- Mayaƙan Dauda suka yi yaƙi gãba da Absalom suka kashe shi. Dauda ya yi baƙinciki da haka ya faru.
(Hakanan duba: Geshur, Amnon)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 03:1-3
- 1 Sarakuna 01:06
- 2 Sama'ila 15:02
- 2 Sama'ila 17:1-4
- 2 Sama'ila 18:18
- Zabura 003:1-2