791 B
791 B
Ibrahim, Ibram
Gaskiya
Ibram mutumin Kaldiya ne daga birnin Ur wanda Allah ya zaɓe shi ya zama kakan Isra'ilawa. Allah ya sauya sunansa zuwa "Ibrahim."
- Ma'anar "Ibram" shi ne "mahaifi da aka ɗaukaka."
- Ma'anar "Ibrahim" shi ne, "mahaifin masu yawa."
- Allah ya yiwa Ibrahim alƙawari zai sami zuriya masu yawa, da za su zama babbar al'umma.
- Ibrahim ya gaskanta Allah ya kuma yi masa biyayya. Allah ya bi da Ibrahim ya tashi daga Kaldiya zuwa ƙasar Kan'ana.
- Lokacin da suke zama a ƙasar Kan'ana, sa'ad da suka tsufa tukuf, Ibrahim da matarsa Saratu suka sami ɗa, shi ne Ishaku.
(Hakanan duba: Kan'ana, Kaldiya, Saratu, Ishaku)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Galatiyawa 03:08
- Farawa 11:29-30
- Farawa 21:04
- Farawa 22:02
- Yakubu 02:23
- Matiyu 01:02