675 B
675 B
Abiyata
Gaskiya
Abiyata babban firist ne domin al'ummar Isra'ila a zamanin Sarki Dauda.
- Sa'ad da Sarki Saul ya kashe firistoci, Abiyata ya kubce ya gudu wajen Dauda a jeji.
- Abiyata da wani firist mai suna Zadok sun bauta wa Dauda da aminci dukkan kwanakin sarautarsa.
- Bayan mutuwar Dauda, Abiyata ya taimaki Adoniya ƙoƙarin ya zama sarki maimakon Suleman.
- Sabili da wannan, Sarki Suleman ya cire Abiyata daga ƙungiyar firistoci.
(Hakanan duba: Zadok, Saul (Tsohon Alƙawari), Dauda, Suleman, Adoniya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 27:32-34
- 1 Sarakuna 01:07
- 1 Sarakuna 02:22-23
- 2 Sama'ila 17:15
- Markus 02:25-26