1.5 KiB
1.5 KiB
alama, alamomi, tabbaci, tunatarwa
Ma'ana
Alama abu ne, ko aiki da kan yaɗa abu mai ma'ana.
- "Tunatarwa" alamomi ne da kan "tunasar" da mutane ta wurin taimakonsu su tuna wani abu, masamman abin da akayi alƙawari:
- Bakangizon da Allah ya halitta a sararin sama alama ne don tunawa jama'a cewa ya yi alƙawari ba zai ƙara hallaka duniya da ruwa ba.
- Allah ya umarci Isra'ilawa da su yiwa'ya'yansu kaciya alamar alƙawarinsa da su.
- Alama kan tona ko ta nuna wani abu:
- Mala'ika ya ba makiyaya alamar da za ta taimakesu su san jaririn da aka haifa mai ceto a Betlehem.
- Yahuda ya simbaci Yesu alamar da shugabannin addini za su gane Yesu domin su kama shi.
- Alamomi kan tabbatar da abin da yake na gaskiya:
- Mu'ujizan da annabawa da manzanni sukayi alamomi ne da suka nuna cewa suna faɗar saƙon Yahweh ne.
- Mu'ujizan da Yesu ya aiwatar suka tabbatar da cewa gaskiya shi ne Almasihu.
Shawarwarin Fassara:
- Ya danganta da nassin, "alama" za a iya fassara ta da "shaida" ko "allon alama" ko "maki" ko "tabbaci" ko " ko"shaida" ko "nuni".
- "Nuna alama da hannuwa" za a iya fassara shi da "motsi da hannu" ko "nuni da hannu" ko "yin nuni."
- A waɗansu yarurrukan, za a iya samun kalma ɗaya domin "alama" da take tabbatar da wani abu da kuma wata kalma daban "alama" da take nufin mu'ujiza.
(Hakanan duba: mu'ujiza, manzanni, Almasihu, alƙawari, kaciya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 02:18-19
- Fitowa 04:8-9
- Fitowa 31:12-15
- Farawa 01:14
- Farawa 09:12
- Yahaya 02:18
- Luka 02:12
- Markus 08:12
- Zabura 089:5-6