1.3 KiB
1.3 KiB
masujada
Ma'ana
kalmar "masujada " na nufin "wuri mai tsarki" yana kuma nuna wurin da Allah ya maida da tsarki da mai tsarki. Haka kuma wurin na nufin wajen bada kariya da mafaka.
- A cikin Tsohon Alƙawari, kalmar "masujada " ana yawan amfani da ita domin a ambaci rumfar sujada ko ginin haikali inda "wuri mai tsarki" da "wuri mafi tsarki" yake.
- Allah ya ambaci masujada a matsayin inda yake zama a tsakanin mutanensa, Isra'ilawa.
- Ya kuma ce da kansa "masujada " ko wuri na tsaro inda mutanensa zasu iya zama ciki.
Shawarwarin Fassara:
- Wannan kalma na da ainihin ma'ana "wuri mai tsaki" ko "wurin da aka keɓe."
- Ya danganta da nassin, kalmar "masujada" za a iya fassarawa haka "wuri mai tsarki" ko "keɓaɓɓen gini" ko " keɓaɓɓen wurin mafaka."
- Faɗar "ma'aunin masujada" za a iya fassarawa haka "wani irin ma'auni da ake bayar wa domin rumfar sujada" ko "ma'aunin da ake amfani da shi wajen biyan haraji domin lura da haikali."
- Lura: Ayi hankali da cewa fassara wannan kalma ba ta da ma'anar ɗakin sujada irin na ikilisiyoyin zamanin yau.
(Hakanan duba: mai tsarki, Ruhu Mai Tsarki, keɓewa, rumfar sujada, haraji, haikali)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Amos 07:13
- Fitowa 25:3-7
- Ezekiyel 25:03
- Ibraniyawa 08:1-2
- Luka 11:49-51
- Littafin Lissafi 18:01
- Zabura 078:69