842 B
842 B
hadayar sulhu
Ma'ana
Wannan magana "hadayar sulhu" yana magana akan hadaya da ake yi domin gamsarwa ko cika adalcin Allah a kuma gamshi fushinsa.
- Baikon hadayar jinin Yesu Almasihu hadayar sulhu ne ga Allah domin zunuban 'yan adam.
- Mutuwar Yesu akan gicciye ya gamshi fushin Allah gãba da zunubi. Wannan ya samar da hanyar da Allah zai dubi mutane da tagomashi ya kuma basu rai madawwami.
Shawarwarin Fassara:
- Wannan magana za a iya fassarawa haka, "gamsarwa" ko "sa Allah ya gafarta zunubai ya kuma yi wa mutane alheri."
- Wannan kalma "kaffara" kusan ma'anarsa ɗaya da "hadayar sulhu." Zai yi kyau idan an auna waɗannan maganganu biyu a ga yadda ake amfani da su.
(Hakanan duba: kaffara, har abada, gafartawa, hadaya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Yahaya 02:02
- 1 Yahaya 04:10
- Romawa 03:25-26