2.2 KiB
2.2 KiB
annabi, annabawa, annabci, yin annabci, mai gani, annabiya
Ma'ana
"Annabi" mutum ne wanda yake faɗin saƙonnin Allah ga mutane. Mace mai yin haka ana kiranta "annabiya."
- Yawancin lokaci annabawa sukan faɗakar da mutane su juyo daga zunubansu su yi biyayya ga Allah.
- "Annabci" shi ne saƙon da annabi ke faɗi. "Yin annabci" shi ne faɗin saƙonnin Allah.
- Yawancin lokaci saƙon annabci na haɗe da abin da zai faru a wani lokaci mai zuwa.
- Annabci da yawa a cikin Tsohon Alƙawari sun rigaya sun cika.
- A cikin Littafi Mai Tsarki, litattafan da annabawa suka rubuta, wasu lokuta ana kiransu "annabawa."
- Misalin wannan furci, "littafin shari'a da annabawa" hanya ce ta ambaton dukkan nassin Yahudawa, waɗanda aka sansu a matsayin "Tsohon Alƙawari."
- Wata tsohuwar magana game da annabi shi ne "mai gani" ko "mutumin dake gani."
- Wani lokaci "mai gani" na nufin maƙaryacin annabi ko wani dake aikata sihiri.
Shawarwarin Fassara:
- Wannan magana "annabi" za a iya fassarawa haka "mai magana ga Allah" ko "mutumin da yake magana domin Allah" ko "mutumin dake faɗar saƙonnin Allah."
- Za a iya fassara "mai gani" haka, "mutumin dake ganin wahayi" ko "mutumin dake hangen lokaci mai zuwa daga Allah."
- Wannan magana "annabiya" za a iya fassarawa haka "mace mai faɗi domin Allah" ko "mace mai magana domin Allah" ko "mace wadda take faɗin saƙonnin Allah."
- Wasu hanyoyin fassara "annabci" za su zama kamar haka, "saƙo daga Allah" ko "saƙon annabi."
- Wannan magana "yin annabci" za a iya fassarawa haka, "faɗin maganganu daga Allah" ko " a faɗi saƙon Allah."
- Wannan misali a cikin furci, "shari'a da annabawa" za a iya fassarawa haka, "litattafan shari'a dana annabawa" ko "dukkan abin da aka rubuta game da Allah da mutanensa, har da shari'ar Allah, da abin da annabawansa suka yi wa'azi a kai."
- Idan ana ambaton annabi (mai gani) na gunki, zai zamana dole a fassara wannan haka "maƙaryacin annabi (mai gani) ko "annabi (mai gani) na gunki" ko "annabin Ba'al," a misali.
(Hakanan duba: Ba'al, sihiri, gunki, maƙaryacin annabi, cika, shari'a, wahayi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tasalonikawa 02:14-16
- Ayyukan Manzanni 03:25
- Yahaya 01:43-45
- Malakai 04:4-6
- Matiyu 01:23
- Matiyu 02:18
- Matiyu 05:17
- Zabura 051:01