844 B
844 B
alƙawari, alƙawarai, alƙawarta
Ma'ana
Alƙawari rantsuwa ce za a yi wani abu. Sa'ad da wani ya yi alƙawarin wani abu, yana nunawa ya bada kai ya yi wannan abu.
- Littafi Mai Tsarki ya rubuta alƙawarai da yawa da Allah ya yiwa mutanensa.
- Alƙawarai mahimman ɓangare ne na yarjejeniyar da aka yi a cikin wa'adodi.
- Yawancin lokaci alƙawari akan haɗa shi da rantsuwa domin a tabbatar za a yi wannan abin.
Shawarwarin Fassara:
- Wannan magana "alƙawari" za a iya fassarawa haka, "miƙa wuya" ko "tabbatarwa" ko "yarjejeniya."
- Idan an yi "alƙawari za a yi wani abu" za a iya fassara ta haka, "ka tabbatar wa wani mutum cewa zaka yi wani abu ko "bada amincewa za a yi abu."
(Hakanan duba: wa'adi, rantsuwa, alƙawari)
- Galatiyawa 03:15-16
- Farawa 25:31-34
- Ibraniyawa 11:09
- Yakubu 01:12
- Littafin Lissafi 30:02