946 B
946 B
Bafarisiye, Farisawa
Ma'ana
Farisawa mahimman mutane ne ƙungiya kuma mai iko na shugabanin addinin Yahudawa a zamanin Yesu.
- Da yawansu mawadatan tsaka-tsaka ne 'yan kasuwa wasunsu kuma firistoci ne.
- Cikin dukkan shugabannin Yahudawa, Farisawa sune masu matsawa ayi biyayya da Shari'ar Musa da kuma wasu dokokin Yahudawa da al'adunsu.
- Suna da damuwar su ga mutanen Yahudawa sun keɓe daga cuɗanya da al'umman dake kewaye da su. Sunan nan "Bafarisiye ya zo ne daga wannan magana "keɓewa."
- Farisawa sun gaskata akwai rayuwa bayan an mutu; kuma sun gaskata akwai mala'iku da wasu hallitun ruhohi.
- Farisawa da Sadusiyawa sun ƙalubalanci Yesu da Kiristocin fãri.
(Hakanan duba: majalisa, shugabannin Yahudawa, shari'a, Sadusiyawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 26:04
- Yahaya 03:1-2
- Luka 11:44
- Matiyu 03:07
- Matiyu 05:20
- Matiyu 09:11
- Matiyu 12:02
- Matiyu 12:38
- Filibiyawa 03:05