2.5 KiB
2.5 KiB
rayuwa, rai, zauna, mai rai, da rai
Ma'ana
Dukkan waɗannan kalmomi na nufin kasancewa da rai a zahiri, ba mutuwa ba. Ana kuma amfani dasu a misali da nufin kasancewa da rai a ruhaniya. Na biye ma'ana "rayuwa a zahiri" da "rayuwar ruhaniya."
- Rayuwa a zahiri
- Rayuwa a zahiri na nufin kasancewar ruhu cikin jiki. Allah ya hura rai a cikin jikin Adamu sai ya zama rayayyen taliki.
- "Rayuwa" kuma na nufin wani taliki a matsayin "an ceto rai."
- Wasu lokutta kalmar "rayuwa" na nufin abin da ake fuskanta a zaman rayuwa, "yana jin daɗin rayuwa."
- Zai iya zama kuma tsawon ran mutum, kamar a bayanin, "ƙarshen rayuwarsa."
- Kalmar nan "mai rai" zai iya kasancewa mai rai a zahiri, a matsayin "mahaifiyata na nan da rai." Zai kuma iya nufin zaunawa a wani wuri kamar, "suna zama a cikin birni."
- A cikin Littafi Mai Tsarki, fannin "rayuwa" yawancin lokaci ana gwada akasinsa da fannin "mutuwa."
- Rai ta Ruhaniya
- Mutum yana da rai ta ruhaniya sa'ad da ya gaskanta da Yesu. Allah yakan ba mutumin nan sabon rai tare da Ruhu Mai Tsarki dake zaune cikinsa.
- Wannan rai kuma ana ce da shi "rai madawwami" domin a nuna baya ƙarewa.
- Akasin rai na ruhaniya shi ne mutuwar ruhaniya, ma'ana rabuwa da Allah da kuma shan hukunci na har'abada.
Shawarwarin Fassara:
- Ya danganta bisa ga nassi, "rai" za a iya fasara shi a ce "zama a raye" ko "mutum" ko "lamiri" ko "wani" ko "ɗanɗanawa."
- Kalmar nan "rayuwa" za a iya fasara ta haka "zama" ko "kasancewa" ko "ana nan."
- Wannan furci "ƙarshen rayuwarsa" za a iya fasara shi zuwa "sa'ad da ya dena rayuwa."
- Wannan furci "an tsare rayukansu" za a iya fasara shi haka "ya bar su su rayu" ko "bai kashe su ba."
- Wannan furci "sun sadakar da ransu" za a iya fasara shi haka "sun sa kansu cikin hatsari" ko "sun yi wani abin da zai iya kashe su.
- Sa'ad da nassin Littafi Mai tsarki yayi magana akan zaman rayayyu a ruhu, za a iya fassara "rayuwa" haka "rayuwar ruhaniya" ko "rai madauwwami" ya danganta ga nassi.
- Wannan furci "rayuwar ruhaniya" za a iya fassarata haka "Allah yakan sa mu zama a raye a ruhohinmu" ko "sabon rai tawurin ruhun Allah" ko "an maida mu rayayyu a cikinmu."
- Ya danganta ga yadda yake a nassi, wannan furci "bada rai" za a iya fassarawa "sa shi ya rayu" ko "bada rai madawwami" ko "sa shi rayu har abada."
(Hakanan duba: mutuwa, har abada)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Bitrus 01:03
- Ayyukan Manzanni 10:42
- Farawa 02:07
- Farawa 07:22
- Ibraniyawa 10:20
- Irmiya 44:02
- Yahaya 01:04
- Littafin Alƙalai 02:18
- Luka 12:23
- Matiyu 07:14