1.2 KiB
1.2 KiB
labari mai kyau, bishara
Ma'ana
Kalmar nan "bishara" ma'anarta ita ce "labari mai kyau" tana kuma nufin saƙo ne ko wani aike da ke faɗawa mutane abin da zai amfane su ya kuma sa su murna.
- A cikin Littafi Mai Tsarki, wanan kalmar har kullum tana magana ne akan aikin ceto na Allah domin mutane ta wurin hadayar Yesu a kan gicciye.
- A cikin mafi yawa daga fassarorin Littafi Mai Tsarki na turanci akan fi fassara ta da "bishara" hakan nan akan mori kalmar "bisharar Yesu Kristi," "bisharar Allah" da kuma "bisharar mulkin."
Shawarwarin Fassara:
- Hanyoyi mabambanta na fassarar wanan kalmar sun haɗa da, "saƙo mai kyau" ko "sanarwa mai kyau" ko "saƙon Allah domin ceto" ko "abu mai kyau da Allah ke koyarwa game da Yesu."
- Ya danganta ga wurin, hanyoyin fassara wanan kalma, "labari mai daɗi na" sun haɗa da, "saƙo mai kyau game da" ko "labari mai daɗi game da" ko "saƙo mai kyau daga" ko "abu mai kyau da Allah ke faɗa mana game da" ko "abin da Allah ke faɗi game da yadda ya ceci mutane."
(Hakanan duba: mulki, hadaya, ceto)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tassalonikawa 01:5
- Ayyukan Manzanni 08:25
- Kolosiyawa 01:23
- Galatiyawa 01:6
- Luka 08:1-3
- Markus 01:14
- Filibiyawa 02:22
- Romawa 01:3