865 B
865 B
bãbã, bãbãni
Ma'ana
A kusan kullum in ana magana akan kalmar nan bãbã ana nufin mutum ne da aka cirewa mazakuta. A wancan lokacin an yi amfani da kalmar wajen ambaton duk wani jami'in gwabnati, koma da waɗanda basu da wani lahani a jiki.
- Yesu ya ce waɗansu bãbãnin haka aka haife su, ƙila sabo da lahani a fannin mazakutarsu, ko kuma sabo da rashin iya yin jima'i. Sauran suka zaɓi yin rayuwa irin ta bãbãni.
- A kwanakin cancan baya bãbãni su ne masu yiwa sarki hidima, akan sa su su zama 'yan tsaro akan wurin zaman mata.
- Waɗansu bãbãnin kuma manyan jami'ai ne na hukuma, irin su bãbã na Habasha, wanda ya sadu da manzo Filib a jeji.
(Hakanan duba: Filib)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 08:27
- Ayyukan Manzanni 08:36
- Ayyukan Manzanni 08:39
- Ishaya 39:7-8
- Irmiya 34:17-19
- Matiyu 19:12