1.1 KiB
1.1 KiB
horarwa, iya horarwa, horarre, horar da kai
Ma'ana
Kalmar nan "horarwa" tana nufin horar da mutane su yi biyayya da waɗansu aiyanannun ka'idoji domin yin rayuwa mai kyau.
- Iyaye kan horar da 'ya'yansu ta wurin gindaya musu sharuɗan rayuwa ta gari da kuma nuna musu yadda za su yi biyayya da wanan koyarwa.
- Hakama Allah kan horar da 'ya'yansa domin taimakon su wajen samun rayuwa ta ruhaniya ingantacciya da za ta bada 'ya'ya a rayuwarsu, kamar farin ciki ƙauna da haƙuri.
- Horarwa ta haɗa da ummarni kan yadda za'a yi rayuwar da zata gamshi Allah, haka nan da hukunci na halaiyar da ta saɓawa nufin Allah.
- Haron kai mataki ne na samar da kuma moron ka'idoji na ruhaniya a cikin rayuwar mutum.
Shawarwarin Fassara:
- Ya danganta da abin da ke wurin horarwa za'a iya fassara ta da "koyo da ba da ummarni" ko "wani nuni na yin rayuwa tagari"ko "ladabtarwa sabo da yin abin da ba dai-da- ba"
- Kalmar "horarwa" za'aiya fassara ta da "horarwa ta halaiya" ko ladabtarwa ko "gyaran hali" ko "nuni kan yin rayuwa tagari."
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Afisawa 06:4
- Ibraniyawa 12:05
- Littafin Misalai 19:18
- Littafin Misalai 23:13-14