1.3 KiB
1.3 KiB
ranar Ubangiji, ranar Yahweh
Ma'ana
A cikin Tsohon Alƙawari "ranar Yahweh" ana ambatonta ne domin a nuna wani lokaci na musamman da Allah zai hukunta mutane sabo da zunubinsu.
- Sabon Alƙawari a yau yana baiyana "ranar Ubangiji" a kan ranar da Yesu zai dawo ya sharianta mutane a ƙarshen lokaci.
- Wannan hukunci na ƙarshe da kuma tashi daga matattu ke tafe shima ana ganinsa a kan "ranar Ubangiji." Wannan lokacin zai fara a lokacin da Yesu zai dawo domin ya shari'anta masu zunubi ya kuma kafa mulkinsa na har abada.
- Kalmar nan "rana" a wasu lokutan ana moron ta domin a nuna wata rana ko kuma wani "lokaci" ko "taro" wanda ya wuce rana ɗaya.
- A wani lokaci kuma ana ganin hukunci akan cewa shi ne "saukar da fushin Allah" a kan waɗanda ba su bada gaskiya ba.
Shawarwarin Fassara:
- Ya danganta ga abin da ke rubuce a wurin, waɗansu hanyoyi da za a fassara "ranar Yahweh" za su iya haɗawa da "lokacin da Yahweh zai hukunta masu ƙin sa" ko kuma "lokacin fushin Yahweh."
- Waɗansu hanyoyi kuma da za a fassara "ranar Ubangiji" sun haɗa da Ubangiji Yesu zai zo ya yi wa duniya shari'a."
(Hakanan duba: rana, ranar hukunci, Ubangiji, tashi daga matattu, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Korintiyawa 05:05
- 1Tassolonikawa 05:02
- 2 Bitirus 03:10
- 2 Tassalonikawa 02:02
- Ayyukan Manzanni 02:20-21
- Filibiyawa 01:9 -11.