1.1 KiB
1.1 KiB
giciye
Ma'ana
A lokacin Littafi Mai Tsarki, giciye wani itace ne da ake soka shi ƙasa, sa'annan a ratsa wani gungume a kusan karshen samansa.
- Lokacin mulkin Romawa, gwamnatin Roma takan kashe masu laifi tawurin tsire su akan giciye a barsu su mutu a nan.
- An zargi Yesu akan laifin da bai yi ba Romawa kuwa suka kashe shi akan giciye.
- A yi lura cewa wannan kalmar dabam take da "tsallakewa" wanda ma'anar ta ƙetarewa ne zuwa wancan hayin, misali, rafi ko tafki.
Shawarwarin Fassara:
- Wannan kalma za a iya fassarata tawurin amfani da wasu magana a harshen masu juyi da ya fassara yadda siffar giciye take.
- Ayi kokarin bayyana yadda giciye yake wato abu ne da ake kashe mutane a kansa, yi amfani da furci haka, "gungumen kisa" ko "itacen mutuwa."
- Yi la'akari da yadda aka fassara wannan kalma a cikin wani Littafi Mai Tsarki na yaren kasar.
(Hakanan duba: gicciyewa, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Korintiyawa 01:17
- Kolosiyawa 02:15
- Galatiyawa 06:12
- Yahaya 19:18
- Luka 09:23
- Luka 23:26
- Matiyu 10:38
- Filibiyawa 02:08