1.7 KiB
1.7 KiB
albarka, mai albarka, sa albarka
Ma'ana
A sã wa wani mutum ko wani abu "albarka" ma'anar shi ne a sã abu mai kyau da abubuwan amfani su faru ga mutumin nan ko wannan abin da ake săwa albarka.
- Ma'anar sã wa wani mutum albarka furta marmarin abu mai kyau da kuma amfani ne ya faru ga mutumin nan.
- A lokacin Littafi Mai Tsarki, yawancin lokaci mahaifi zai furta ƙaiyadadden albarka akan yaransa.
- Sa'ad da mutane suka "albarkaci" Allah ko suka nuna son a albarkaci Allah, wannan ya nuna suna yabon sa.
- Wannan kalma "albarka" wani lokaci ana amfani da ita a tsarkake abinci kafin a ci ko domin godiya da kuma yabon Allah domin abincin.
Shawarwarin Fassara:
- Idan an sã "albarka" za a iya fassara shi ya zama "ayi tanadi mai ɗunbun yawa domin" ko "ayi alheri da tagomashi ga."
- "Allah ya kawo babbar albarka ga" za a iya juya shi haka, "Allah ya bada kyawawan abubuwa da yawa ga" ko "Allah yayi tanadi jingim domin" ko "Allah ya sa abubuwa masu kyau su faru."
- "An albarkace shi" za a iya juya shi haka "Zai sami babbar riba" ko "zai ɗanɗana abubuwa masu kyau" ko "Allah zai sa ya wadata."
- "Mai albarka ne mutumin da" za a iya fasara shi haka "Zai zama da kyau ƙwarai ga mutum wanda."
- Furci kamar wannan "albarka ga Ubangiji" za a iya fasarata "Bari a yabi Ubangiji" ko "Yabi Ubangiji" ko "Na yabi Ubangiji."
- A lokacin da aka sã wa abinci albarka, za a iya fassara wannan haka, "a gode wa Allah domin abinci" ko "a yabi Allah domin ya basu abinci" ko "a tsarkake abincin ta wurin yabon Allah domin sa.
(Hakanan duba: yabo)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Korintiyawa 10:16
- Ayyukan Manzanni 13:34
- Afisawa 01:03
- Farawa 14:20
- Ishaya 44:03
- Yakubu 01:25
- Luka 06:20
- Matiyu 26:26
- Nehemiya 09:05
- Romawa 04:09