1.3 KiB
1.3 KiB
iko, hukuma, ikoki
Ma'ana
Wannan kalma "iko" fassararta shi ne karfin bishewa da mallaka da wani mutum yake da shi akan wani mutum daban.
- Sarakai da masu sarauta suna da iko akan mutanen da suke mulki.
- Kalman nan "mulkoki" yana nufin mutane, gwamnatai, ko ƙungiyoyi da suke da iko kan wasu.
- Maigida yana da iko akan barorinsa ko bayi. Iyaye suna da iko akan 'ya'yansu.
- Gwamnati tana da iko ko 'yanci ta kafa dokoki da zasu kare 'yan ƙasarta.
Shawarwarin Fassara:
- Wannan kalma "iko" za a iya fassarata haka, "sarrafa" ko "'yanci" ko "fannin ƙwarewa."
- Wani lokaci "iko" zai iya zama da ma'ana haka "ƙarfi."
- Sa'ad da aka yi amfani da "masu iko" game da mutane ko ƙungiyoyi dake mulkin mutane, za a iya fasara shi a ce "shugabanni" ko "masu mulki" ko "ikoki."
- Wannan faɗar "da ikon kansa" za a iya juya shi a ce "da 'yancin kansa na shugabanci" ko "bisa ga fannin kwarewarsa."
- Wannan furci "ƙarƙashin iko" za a iya fassara shi haka, "yana da kamun kai yayi biyayya." ko "yana biyayya da umarnan waɗansu."
(Hakanan duba: ɗan ƙasa, umarni, biyayya, iko mai mulki)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Kolosiyawa 02:10
- Esta 09:29
- Farawa 41:35
- Yona 03:6-7
- Luka 12:05
- Luka 20:1-2
- Markus 01:22
- Matiyu 08:09
- Matiyu 28:19
- Titus 03:01