ha_tw/bible/kt/highpriest.md

37 lines
1.8 KiB
Markdown

# babban firist, shugabannin firistoci
## Ma'ana
Kalmar nan "babban firist" tana nufin firist na musamman da aka sa ya yi hidimar babban firist na shekara ɗaya a matsayin shugaban dukkan firistocin Isra'ila. A lokacin Sabon Alƙawari, waɗansu sauran firistocin suma akan ɗauke su da muhimmanci sosai a cikin shugababannin addinin Yahudawa, tare da iko akan sauran firistocin da kuma mutane. Waɗannan su ne manyan firistoci.
* Babban firist na da aikin na musamman. Shi kaɗai ke da damar shiga wuri mafi tsarki na rumfar sujada ko haukali domin miƙa hadaya sau ɗaya a shekara.
* Isra'ilawa na da firistoci da yawa, amma babban firist ɗaya ne tak a lokaci guda.
* Bayan babban firist ya yi ritaya, sukan riƙe sunan matsayinsu, tare da sauran waɗansu aikace-aikace na ofishi. Misali, Annas ya kasance babban firist a lokacin aikin firist na Kayafas da sauransu.
* Manyan firistoci su ke da ɗawainiyar duk wani abu da ya shafi sujada a cikin haikali. Hakanan su ne ke kula da kuɗi da aka bayar a cikin haikali.
* Manyan firistoci su ne suka fi girma da iko fiye da sauran firistoci. Babban firist ne kaɗai ya fi iko.
* Shugabannin firistoci su ne suka zama waɗansu daga cikin manyan maƙiyan Yesu kuma suka matsa wa shugabannin Romawa da su kama shi su kashe shi.
Shawarwarin Fassara:
"Babban firist" za'a iya fassara shi da "firist mafi iko" ko " firist mafi girman matsayi."
* Kalmar nan "manyan firistoci" za'a iya fassara ta da "shugabannin firistoci" ko "jogororin firistoci" ko "mahukuntan firistoci."
(Hakanan duba: Annas, Kayafas, firist, haikali)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
* Ayyukan Manzanni 05:27
* Ayyukan Manzanni 07:1
* Ayyukan Manzanni 09:1
* Fitowa 30:10
* Ibraniyawa 06:19-20
* Lebitikus 16:32
* Luka 03:2
* Markus 02:25-26
* Matiyu 26:3-5
* Matiyu 26:51-54