1.3 KiB
1.3 KiB
shiƙa, sheƙewa, an sheƙe, ana sheƙewa, bakace, bakacewa
Ma'ana
Kalmar "shiƙa" da "tankaɗe" na manufar raba hatsi daga kayayyakin da ba a so. A Littafi Mai Tsarki, kalmomin biyu ana amfani da su a bayyana rabawa ko wãre mutane.
- A yi "shiƙa" na nufin a raba hatsi daga sauran sashen hatsin da basu da amfani ta kaɗa hatsin da ƙaiƙayin cikin iska, iskar tana hurar da ƙaiƙayin.
- Kalmar "bakace" na bayyana kakkaɓe hatsin da aka yi shiƙarsa cikin abin bakacecewa domin a cire sauran abubuwan da ba a buƙata, kamar datti ko duwatsu.
- A cikin Tsohon Alƙawari, "shiƙa" da "bakace" ana amfani da su ne a bayyana shan wuyar dake banbanta tsakanin adalai da marasa adalci.
- Yesu ya yi amfani da kalmar "sheƙewa" yayin da yake faɗi wa Siman Bitrus yadda za a gwada bangaskiyarsa da na sauran almajiran.
- A fassarar waɗannan kalmomin, ayi amfani da kalmomi ko faɗar a cikin yare da ake aiki a kai dake ma'anar waɗannan ayyuka; wasu fassarorin masu yiwuwa su ne "girgiza" ko "tankaɗe." Idan ba a san shiƙa ko bakace ba, daga nan waɗannan kalmomi za a iya fassara su ta wurin kalmar dake ma'anar hanya daban-daban ta rarrabe hatsi daga ƙaiƙayi ko datti, ko ta wurin bayyana wannan aikin.
(Hakanan duba: ƙaiƙayi, hatsi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ishaya 21:10
- Luka 22:31
- Matiyu 03:12
- Littafin Misalai 20:08
- Rut 03:02