815 B
815 B
matatsar ruwan inabi
Ma'ana
A kwanakin Littafi Mai Tsarki, "matatsar ruwan inabi" babbar gidauniya ce ko wuri ne mai faɗi inda ake tatsar 'ya'yan itacen inabi domin samun ruwan inabi.
- A Isra'ila, matatsun ruwan inabi wurare ne masu girma, manyan darurukan da aka sassaƙo daga dutse. Curin 'ya'yan itacen inabi za a zuba su mutane su tattake da kafafunsu ruwan inabin na zubowa.
- Akwai matakai guda biyu, sama da ƙasa da ake zuba 'ya'yan itacen inabin domin a tattake su daga sama ruwan na zubowa a sashe na ƙasa inda ake tarawa.
- "Matatsar inabi" ana amfani da ita a nuna bayyanuwar hasala da fushin Allah da ake kwararowa bisa mugayen mutane.
(Hakanan duba: itacen inabi, hasala)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ishaya 63:02
- Markus 12:01
- Matiyu 21:33
- Wahayin Yahaya 14:20