852 B
852 B
alkama
Ma'ana
Alkama wani irin hatsi ne da mutane ke shukawa domin abinci. A duk lokacin da Littafi ya ambaci "hatsi" ko "iri," yawancin lokuta ana manufar alkama ne ko ƙwayar iri.
- Ƙwayar irin alkama ko hatsi na tsirowa ne a bisa kan dashen.
- Bayan an girbe alkamar, ana rarrabe hatsin daga zangarniyar ta wurin sussukewa. Kan dashen alkamar ana kiransa da suna "haki" kuma ana zuba su a ƙasa domin dabbobi su kwanta bisa.
- Bayan sussuka, ƙaiƙayin dake zagaye da irin ana rarrabe su daga hatsin ta wuri sheƙewa a kuma zubar da shi.
- Mutane na niƙa tsabar alkama zuwa gãri, su kuma yi amfani da ita wurin yin gurasa.
(Hakanan duba: bali, ƙaiƙayi, hatsi, iri, sussuka, shiƙa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 27:36-38
- Fitowa 34:21-22
- Yahaya 12:24
- Luka 03:17
- Matiyu 03:12
- Matiyu 13:26