1.2 KiB
1.2 KiB
gyale, gyalulluka, lulluɓewa, kware lulluɓi
Ma'ana
Kalmar "gyale" na bayyana wata sutura marar kauri da ake amfani da ita domin rufe kai, a rufe kai ko fuska domin kada a ganta.
- Musa ya rufe fuskarsa da gyale bayan da ya zauna a gaban Yahweh, domin walƙiyar fuskarsa shi ɓoyu ga mutanen.
- A cikin Littafi Mai Tsarki, mataye suna rufe kansu da gyale, lokatai da dama kuma har da fuskarsu, idan suna cikin mutane ko inda mazaje suke.
- Kalmar aiki "gyale" na nufin a rufe wani abu da gyale.
- A wasu fassarorin, kalmar "gyale" ana morarsu a kira labule mai kauri da ya rufe mashigin wuri mafi tsarki. Amma "labule" yafi dai-dai a yi amfani da shi a wannan nassin, domin yana da kauri, yadi mai kauri.
Shawarwarin Fassara:
- Kalmar "gyale" za a iya fassarawa haka "suturar lulluɓewa marar kauri" ko "suturar lulluɓewa" ko "abin lulluɓe kai."
- Wasu al'adun, za ya iya kasancewa suna da kalmar gyale domin mata. Zai zama da muhimmanci a sami wata kalmar daban idan za a yi amfani da ita game da Musa.
(Hakanan duba: Musa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Korintiyawa 03:12-13
- 2 Korintiyawa 03:16
- Ezekiyel 13:18
- Ishaya 47:1-2
- Waƙar Suleman 04:3