787 B
787 B
fahimta, fahimci, gane, fahimtar, tunani
Ma'ana
Kalmar "fahimta" na manufar a ji ko karɓar bayani a san me yake nufi.
- Kalmar "fahimci" na iya nufin "ilimi" ko "hikima" ko ganewa yadda za a iya yin wani abu.
- A fahimci wani na nufin a san yadda wannan mutum ke ji.
- Sa'ad da yake tafiya kan hanya zuwa Imawus, Yesu ya sa almajiran suka fahimci ma'anar nassin game da Almasihu.
- Ya danganta da nassin, kalmar "fahimta" ana iya fassararta haka "sani" ko "yarda" ko "sasancewa" ko "a san menene ma'anar wani abu."
- Yawanci kalmar "fahimta" ana iya fassara ta da cewa "ilimi" ko "hikima" ko "zurfi."
(Hakanan duba: bangaskiya, sani, mai hikima)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayuba 34:16-17
- Luka 02:47
- Luka 08:10
- Matiyu 13:14
- Littafin Misalai 03:05