778 B
778 B
ƙaho, ƙahonni, mabusa ƙaho, kakaki, kakakai, mabusa kakaki
Ma'ana
Kalmar "ƙaho" na nufin wani abu dake fitar da busa ko domin kiran mutane su tattaru tare domin wata sanarwa ko taro.
- Shi dai ƙaho ko kakai ana yinsa daga ko dai ƙarfe, koɗin dabbar teku, ko ƙahon dabba.
- Ƙahonni ko kakakai su dai busa su ake yi a kira mutane su zo su taru domin yaƙi, da kuma tarurrukan Isra'ilawa a fili.
- Littafi Wahayin Yahaya ya yi bayanin kasancewar a lokutan ƙarshe inda mala'iku suka busa ƙahonni su bada alamar zubowar hasalar Allah bisa duniya.
(Hakanan duba: mala'ika, taro, duniya, ƙaho, Isra'ila, hasala)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 13:7-8
- 2 Sarakuna 09:13
- Fitowa 19:12-13
- Ibraniyawa 12:19
- Matiyu 06:02
- Matiyu 24:31