775 B
775 B
tsanani, ƙunci, matsala
Ma'ana
Kalmar "tsanani" na nufin lokacin shan wuya, wahala, da ƙunci.
- Anyi bayanin ta a Sabon Alƙawari cewa Kiristoci zas jure lokutan wahalhalu da sauran tsanani daban-daban saboda mutane da yawa a wannan duniya suna tsayayya da koyarwar Yesu.
- "Babban Tsanani" kalma ce da ake amfani da ita a Littafi Mai Tsarki ayi bayanin wani zamani gab da zuwan Yesu karo na biyu sa'ad da fushin Allah zai zubo bisa duniya na shekaru da yawa.
- Kalmar "tsanani" za a kuma iya fassarawa haka "lokacin babbar wahala" ko "ƙunci mai zurfi" ko "wahalhalu masu tsanani."
(Hakanan duba: duniya, koyarwa, hasala)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Markus 04:17
- Markus 13:19
- Matiyu 13:20-21
- Matiyu 24:09
- Matiyu 24:29
- Romawa 02:09