1.1 KiB
1.1 KiB
azaba, azabta, azabtarwa, masu azabtarwa
Ma'ana
Kalmar "azaba" na nufin tsanantacciyar wahala. A azabtar da wani na nufin a sa wannan taliki ya sha wuya ta hanyar tsananin mugunta.
- Wasu lokuta kalmar "azaba" na nufin jin zafi da wahala a zahiri. A misali, littafin Wahayin Yahaya ya bayyana irin azaba a zahiri da masu sujada ga "bisan" zasu sha a zamanin ƙarshe.
- Shan wuya kuma na iya ɗaukar kamanni a zafi a ruhaniya da lamiri, kamar yadda Ayuba ya fuskanta.
- Manzo Yahaya ya rubuta a Littafin Wahayin Yahaya cewa mutanen da basu bada gaskiya ga Yesu ba a matsayin mai ceton su zasu fuskanci azaba ta har abada a cikin ƙoramar wuta.
- Wannan kalma za a iya fassarawa haka "tsanantacciyar wahala" ko "sanya wani ya sha wuya mai girma" ko "tsananin zafi." Wasu masu fassarar za su iya ƙara "a zahiri" ko "a ruhaniya" domin a fayyace ma'anar.
(Hakanan duba: bisan, har abada, Ayuba, Mai ceto, ruhu, wahala, sujada)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Bitrus 02:08
- Irmiya 30:20-22
- Littafin Makoki 01:11-12
- Luka 08:28-29
- Wahayin Yahaya 11:10