1.3 KiB
1.3 KiB
lokaci, kan lokaci, lokuta, kafin lokaci, rana
Ma'ana
A cikin Littafi Mai Tsarki kalmar "lokaci" anyi yawan amfani da ita a matsayin misali dake nufin wani ainihin zamani ko lokaci sa'ad da wasu al'amura suka faru. Tana da ma'ana kusan ɗaya da "shekara" ko "lokacin tarihi" ko "zamani."
- A cikin Daniyel duk da Wahayin Yahaya maganar "lokacin" babban ƙalubale ko tsanani wanda zai zo bisa duniya.
- A cikin faɗar "lokaci, lokuta, da rabin lokaci" kalmar "lokaci" na ma'anar "shekara." Wannan faɗar na nufin lokaci shekaru uku da rabi a lokacin babban tsanani a ƙarshen wannan zamanin.
- "Lokaci" na iya zama "zarafi ko karo" a faɗar kamar haka "kokaci na uku." Faɗar "lokuta da yawa" zai iya zama "zarafi ko karo."
- A zama "kan lokaci" na ma'anar a iso lokacin da ake zato, babu latti.
- Ya danganta da nassin, kalmar "lokaci" za a iya fassarawa haka, "zamani" ko "lokacin sa'a" ko "lokacin" ko "faruwa."
- Faɗar "lokuta da zamanai" faɗar misali ne wanda ke manufar abu ɗaya aka maimaita sau biyu. Wannan shima za a fassara haka "wasu abubuwa na faruwa a wani lokacin sa'o'i."
(Hakanan duba; shekara, tsanani)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 01:07
- Daniyel 12:1-2
- Markus 11:11
- Matiyu 08:29
- Zabura 068:28-29
- Wahayin Yahaya 14:15