888 B
888 B
kursiyi, kursiyoyi, ɗorawa bisa kursiyi
Ma'ana
Kursiyi wata kujera ce da aka sassaƙa musamman inda mai mulki ke zama sa'ad da yake ɗaukar matakai akan muhimman al'amura kuma yake sauraren roƙe-roƙe daga mutanensa.
- Kursiyi kuma alama ne na hukunci da iko da mai mulki ke da shi.
- Kalmar "kursiyi" yawanci ana amfani da ita a misali da ma'anar mai mulki, mulkinsa, ko ikonsa.
- A cikin Littafi Mai Tsarki, ana yawan bayyana Allah a matsayin sarki dake zaune akan kursiyi. Ana bayyana Yesu na zaune a bisa kursiyi a hannun dama na Allah Uba.
- Yesu yace sama kursiyin Allah ne. Hanya ɗaya ta fassara wannan zata iya zama, "inda Allah yake mulki a matsayin sarki."
(Hakanan duba: hukunci, iko, sarki, mulki)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Kolosiyawa 01:15-17
- Farawa 41:40
- Luka 01:32
- Luka 22:30
- Matiyu 05:34
- Matiyu 19:28
- Wahayin Yahaya 01:4-6