1.1 KiB
1.1 KiB
ƙaya, sarƙaƙiyar ƙaya, ƙayayuwa, furen ƙaya, furannin ƙaya
Ma'ana
Sarƙaƙiyar ƙaya da furannin ƙaya dukka tsire-tsire ne ko 'yan itatuwa da suke da rassa ko furannin ƙaya. Waɗannan itatuwa basu haifar da 'ya'ya ko wani abin amfani.
- "Ƙaya" wani abu ne mai tsini da ƙarfi dake fitowa a jikin reshe ko jikin itacen. "Sarƙaƙiyar ƙaya" wani irin ƙaramin itace ne ko tsiro wanda keda ƙayayuwa da yawa a rassansa.
- "Furen ƙaya" itace ne dake da rassa masu ƙai-ƙai da ganyaye. Yawanci kalar furannin shunayya ne.
- Itatuwan sarƙaƙiyar ƙaya da furen ƙaya suna ruɓanɓanya da sauri su kuma sa sauran itatuwa da shuke-shuke dake kusa da su su kasa yin girma. Wannan hoto ne na yadda zunubi ke hana wani taliki haifar da kyawawan 'ya'yan ruhaniya.
- Kambin da aka yi da naɗaɗɗun rassan ƙaya aka ɗora bisa kan Yesu kafin a gicciye shi.
- Idan mai yiwuwa ne, waɗannan kalmomi za a fassara su da sunayen itatuwa biyu daban ko sarƙaƙiyu da aka san su a yaren wurin.
(Hakanan duba: kambi, 'ya'yan itace, ruhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ibraniyawa 06:7-8
- Maityu 13:07
- Maityu 13:22
- Littafin Lissafi 33:55