739 B
739 B
rumfar taruwa
Ma'ana
Kalmar "rumfar taruwa" na nufin wata rumfa ce wadda aka kafa na ɗan lokaci inda Allah ke haɗuwa da Musa kafin a kafa rumfar sujada.
- An kafa rumfar taruwa waje da sansanin Isra'ilawa.
- Sa'ad da Musa ya shiga rumfar taruwa domin ya gamu da Allah, ginshikin girgije zai tsaya a bakin kofar shiga rumfar a matsayin alamar kasancewar Allah a wurin.
- Bayan da Isra'ilawa suka kafa rumfar sujada, waccan rumfar ba a buƙatar ta kuma sai kalmar "rumfar taruwa" wasu lokuta ana amfani da ita da nufin rumfar sujada.
(Hakanan duba: Isra'ila, Musa, ginshiƙi, rumfar sujada, rumfa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sarakuna 02:28-29
- Yoshuwa 19:51
- Lebitikus 01:02
- Littafin Lissafi 04:31-32