1.0 KiB
1.0 KiB
malami, malamai, Malami
Ma'ana
Malami wani taliki ne dake bayar da sabobbin labarai ga mutane. Malamai suna taimakawa mutane su sami ilimi da fasaha.
- A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar "malami" ana amfani da ita da manufa ta musamman a nuna wani dake koyarwa game da Allah.
- Mutanen dake koyo daga malami ana kiransu "ɗalibai" ko "almajirai."
- A wasu fassarorin Littafi Mai Tsarki, ana amfani da babban harafi ("Malami") sa'ad da aka yi amfani da laƙabin ga Yesu.
Shawarwarin Fassara:
- Kalmar da aka saba da ita ta malami za a iya amfani da ita wajen fassara wannan kalma, sai dai idan kalmar domin malamin makaranta ne kawai ake amfani da ita.
- Wasu al'adun na iya kasancewa da wani laƙabi na musamman domin malaman addini, kamar su "Yallaɓai" ko "Rabbi" ko "Mai Wa'azi."
(Hakanan duba: almajiri, wa'azi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Littafin Mai Wa'azi 01:12-15
- Afisawa 04:11-13
- Galatiyawa 06:6-8
- Habakuk 02:18
- Yakubu 03:02
- Yahaya 01:37-39
- Luka 06:40
- Matiyu 12:38-40