1.4 KiB
1.4 KiB
koyawa, koyarda, koya, koyarwa, marar koyarwa
Ma'ana
A "koyawa" wani shi ne a gaya masa wani abu da bai riga ya sani ba. Yana kuma iya nufin "a wadatar da labarai" a taƙaice, ba tare da ambaton wanda ke koyon ba. Yawanci ana bada labarai ta hanya dai-daitacciya ko bisa tsari. Mai "koyawa" ko "koyarwar" sa sune abin da yake koyarwa.
- Shi "malami" wani ne mai koyarwa. "Koyar" da abin da ya wuce shi ne "koya."
- Sa'ad da Yesu yake koyarwa, yana bayanin abubuwa game da Allah da mulkinsa.
- Almajiran Yesu na kiransa "Malami" a matsayin nuna bangirma ga wanda yake koyarwa game da Allah.
- Abin da ake koyarwa za a iya nuna wa ko magana akai.
- Kalmar "koyarwa" na nufin jerin koyarwa daga Allah game da shi kansa da kuma umarnan Allah game da yadda za a yi rayuwa. Za a iya fassara wannan ma a matsayin "koyarwa daga Allah" ko "abin da Allah yake koyarwa."
- Faɗar "abin da kuka koya" za a iya fassarawa kuma, "abin da waɗannan mutane suka koyar daku" ko "abin da Allah ya koyar daku," ya danganta da nassin.
- Wasu hanyoyin fassara "koyawa" sun haɗa da a "faɗi" ko ayi "bayani" ko bada "umarni."
- Yawanci ana fassara wannan kalma a matsayin "koyawa mutane game da Allah."
(Hakanan duba: umarni, malami, maganar Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Timoti 01:03
- Ayyukan Manzanni 02:40-42
- Yahaya 07:14
- Luka 04:31
- Matiyu 04:23
- Zabura 032:08