1.3 KiB
1.3 KiB
wuya, barni, wahaloli, shan wuya, sha wuya, shan wahala
Ma'ana
Kalmar "wuya" da "wahala" na nufin fuskantar wani abu marar daɗi, kamar rashin lafiya, tsanani, ko wata damuwa.
- Idan ana tsanantawa mutane ko idan basu da lafiya, suna shan wuya.
- Wasu lokutan mutane na shan wuya saboda abubuwa marasa kyau da suka yi; a wasu lokutan sukan sha wuya saboda zunubi da cuta a duniya.
- Wahala na iya zama a jiki, kamar jin zafi ko rashin lafiya. Yakan iya zama a cikin tunani, kamar jin tsoro, ɓacin rai, ko kaɗaici.
- Kalmar "barni" na nufin "yi hakuri dani" ko "ka saurare ni" ko "yi hakurin sauraro."
Shawarwarin Fassara:
- Kalmar "wuya" akan fassarata da "jin zafi" ko "jurewa wahala" ko "jin damuwoyi" ko "shiga cikin tsanani da jin zafi."
- Ya danganta da nassin, "wahala" akan fassara ta da "yanayi mai tsananin wahala" ko "damuwa ta gaske" ko "ɗanɗana matsala" ko "lokacin ɗanɗana tsanani."
- Kalmar "wuyar ƙishi" akan fassara ta da "ɗanɗana ƙishi" ko "shan wahalar ƙishi."
- "Wahalar rikici" akan iya fassara shi da "fuskantar rikici" ko "cutuwa ta dalilin rikici."
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tasalonikawa 02:14-16
- 2 Tasalonikawa 01:3-5
- 2 Timoti 01:08
- Ayyukan Manzanni 07 :11-13
- Ishaya 53:11
- Irmiya 06:6-8
- Matiyu 16:21
- Zabura 022:24
- Wahayin Yahaya 01:09
- Romawa 05:3-5