815 B
815 B
abin sha mai ƙarfi, abubuwan sha masu ƙarfi
Ma'ana
Wannan kalma "abin sha mai ƙarfi" na nufin abubuwan shan da aka gauraya suka zama giya a cikin su.
- Giya akan yi tane daga kodai hatsi ko 'ya'yan itace da suke kaiwa ga harzaƙuwa.
- Irin wannan "abin sha mai ƙarfin" sun haɗa da ruwan inabi, bammi, giya, da tuffar sida. A Littafi Mai Tsarki, ruwan inabi aka fi ambata a kowanne abin sha.
- Firistoci da kowanne mutum da ya yi wata rantsuwa ta masamman kamar ta "ranzuwar Banaziri ko Naziranci" ba a basu izinin shan gaurayayyun abubuwan sha ba.
- Wannan kalmar akan iya fassara ta da "gaurayayyen abin sha" ko "ruwan giya."
(Hakanan duba: inabi, Banaziri, rantsuwa, giya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ishaya 05:11-12
- Lebitikus 10:09
- Luka 01:14-15
- Littafin Lissafi 06:03