898 B
898 B
martaba
Ma'ana
Kalmar "martaba" na nufin matuƙar kyau da gayu da a koda yaushe yake da nasaba da wadata da fita ta alfarma.
- Koyaushe akan yi amfani da ado mai martaba a nuna wadatar da sarki yake da ita, ko yadda yake a cikin kayan adonsa masu tsada.
- Kalmar "martaba" kan iya amfani wajen bayyana kyan bishiyoyi, duwatsu, da sauran abubuwa da Allah ya halitta.
- Garuruwa da dama ana cewa suna da martaba saboda ma'adanan da suke da su suna bunƙasa gine-gine da hanyoyi, da kuma dukiyar jama'arsu,wadda ta haɗa da tufafi mai tsada, gwal zinariya da azurfa.
- Ya danganta da nassin, za a iya fassara wannan kalmar da "kyau mai kayatarwa" ko "daraja mai ban mamaki" ko "girman sarauta."
(Hakanan duba: ɗaukaka, sarki, daraja)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 16:27
- Fitowa 28:1-3
- Ezekiyel 28:07
- Luka 04:07
- Zabura 089:44-45
- Wahayin Yahaya 21:26-27