1.1 KiB
1.1 KiB
yanka, yankewa, yankawa
Ma'ana
Kalmar " yanka" na nufin kashe dabbobi da yawa ko mutane, ko kashewa ta hanyar tashin hankali. Yana kuma iya zama kashe dabbobi domin ci. Yin aikin yanka shi ake nufi da "yankawa."
- Lokacin da Ibrahim ya karɓi baƙuncin bãƙi guda uku gidansa a daji, ya umarci baransa ya yanka ya kuma girka bijimi domin bãƙinsa.
- Annabi Ezekiyel ya yi anabci cewa Yahweh zai aiko da mala'ikansa ya yayyanka duk wanda ya ƙi bin maganarsa.
- 1 Sama'ila ya rubuta wani gagarimin yanka da akayi inda aka kashe Isra'ilawa guda 30,000 ta hannun maƙiyansu saboda rashin biyayya ga Yahweh.
- "Makamin yanka" za a iya fassara shi da " makamin kisa."
- Faɗar "yankan yana da girma" akan iya fassara shi da " dayawa aka yanka" ko yawan waɗanda suka mutu na da yawa" ko " mutanen da suka mutu na da matuƙar yawa."
- Waɗansu hanyoyin da akan iya fassara "yanka" sun haɗa da "kisa" ko "hallakawa" ko " kashewa."
(Hakanan duba: mala'ika, saniya, rashin biyayya, Ezekiyel, bara, yankawa)
Wuraren da akan samesa a Littafi Mai Tsarki:
- Ezekiyel 21:10-11
- Ibraniyawa 07:01
- Ishaya 34:02
- Irmiya 25:34