894 B
894 B
baikon zunubi, baye-baye na zunubi
Ma'ana
"Baikon zunubi" na daga cikin hadayu da Yahweh ya umarci Isra'ila su yi.
- Wannan baikon ya haɗa da hadayar maraƙi, a ƙona jininsa da kitsensa a kan bagadi, a kuma ɗauki sauran jikin dabbar a ƙone ta a wajen sansanin Isra'ilawa.
- Dukkan ƙone wannan dabbar na nuna yadda Yahweh ya je da tsarki da kuma yadda zunubi yake da razanarwa.
- Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa idan ana so a tsarkaka daga zunubi, dole a zub da jini don ya biya tamanin zunubin da akayi.
- Hadaya da dabba bazai kawo gafarar zunubi ta har abada ba.
- Mutuwar Yesu akan gicciye ta biya hukuncin zunubi, na dukkan lokaci. Shi ne cikakken baikon zunubi.
(Hakanan duba: bagadi, saniya, gafara, hadaya, zunubi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Tarihi 29:20-21
- Fitowa 29:35-37
- Ezekiyel 44:25-27
- Lebitikus 05: 11
- Littafin Lissafi 07:15-17