1.5 KiB
1.5 KiB
dangantaka da, yin soyayya, kwanta da, kwana da, kwanciya da
Ma'ana
A cikin Littafi Mai Tsarki, waɗannan kalmomin an jaddadasu da suke nuna yin jima'i.
- Maganar "kwana da" wani yana nuna yin jima'i da wannan mutumin. idan ya wuce shi ne "kwanta da."
- A littafin tsohon alƙawari "waƙar suleman", an yi amfani da kalmar " yin soyayya" don fassara kalmar "ƙauna", wanda a nassin ake maganar yin jima'i. Wannan na da dangantaka da maganar "soyayya da wani".
Shawarwarin Fassara:
- Waɗansu yarurrukan na iya amfani da maganganu daban-daban ga wannan magana a matakai daban-daban, ya danganta ko waɗanda abin ya shafa ma'aurata ne ko kuma suna da wata dangantaka. Yana da mahimmanci a tabbatar da cewa fassarar wannan magana tana da ma'ana mai kyau a kowanne mataki.
- Ya danganta ga fannin, maganganu kamar waɗannan akan iya amfani da su a fassara "kwana da": "kwanciya da" ko "yin soyayya" ko "kusanci da".
- Waɗansu hanyoyin yin fassarar kuma "samun dangantaka da " kan haɗa da "samun dangantakar yin jima'i da" ko "samun dangantakar aure da".
- Kalmar " yin soyayya" akan iya fassara ta da "ƙaunar" ko "kusanci". ko kuma akwai wata magana da take ta ainahi da kan fassara wannan a cikin yaren da ake aiki da shi.
- Yana da mahimmanci a duba abin da aka mora wajen fassara wannan abin su zama amintattu ga jama'ar da za su yi amfani da wannan fassarar Littafi Mai Tsarki.
(Hakanan duba: aikin lalata)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Korintiyawa 05:1-2
- 1 Sama'ila 01:19
- Maimaitawar Shari'a 21:13
- Farawa 19:05
- Matiyu 01:25