1.1 KiB
1.1 KiB
Aike, Aiko, aikawa, aika waje, aikawa waje
Ma'ana
A "aike" shi ne sa wani ko wani abu ya je wani wuri. A "aika waje" na nufin wani ya ce da wani ya je aike ko wata manufa.
- A koyaushe mutum wanda aka "aika" ansa shi ne ya yi wani aiki na masamman.
- Magana kamar " aika ruwa" ko "aika annoba" na nufin "la'anta ta zo". Wannan irin maganar anfi amfani da ita akan Yahweh ne yake sa wannan ya auku.
- Kalmar " aike" akan yi amfani da ita wurin magana kamar " aika magana" ko A "aika sako," wanda yake nufin ba wani sako ya gayawa wani.
- A "aika" wani da "wani" abu na nufin "abã" da wannan abin ga wani ya "bã" wani, akan aika wannan da nisa domin wani ya karɓa
- Yesu lokuta da dama ya yi amfani da wannan maganar " wanda ya aiko ni" yana nufin Yahweh Uba wanda ya, "aiko" shi duniya don ceton mutane. Wannan ma a fassara shi kamar wanda ya bada kai.
(Hakanan duba: zaɓa, fansa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 07:33-34
- Ayyukan Manzanni 08:14-17
- Yahaya 20:21-23
- Matiyu 09:37-38
- Matiyu 10:05
- Matiyu 10:40
- Matiyu 21:1-3