1014 B
1014 B
naɗaɗɗen littafi, naɗaɗɗun litattafai
Ma'ana
A zamanin dã, naɗaɗɗen littafi wani irin littafi ne dake da tsayi, naɗaɗɗe ne daga fafirus ko fãta.
- Bayan an yi rubutu a bisa naɗaɗɗen littafi ko an yi karatu daga cikinsa, mutane suna naɗe shi ta wurin yin amfani da ƙarafunan dake harɗe da iyakarsa.
- Naɗaɗɗun litattafai ana amfani da su domin ajiye rubutun dokoki da littafi mai tsarki.
- Wasu lokuta naɗaɗɗun litattafan da ɗan saƙo ke kawo wa ana bugawa da hatimi na kakin zuma ko ƙaro. Idan kakin zuma ƙaron na a ɗanyensa a lokacin da aka kawo saƙon, da haka shi mai karɓar saƙon zai san da cewa ba a buɗe wannan naɗaɗɗen littafi,ba ko a yi rubutu cikinsa ba tunda an riga an hatimce shi.
- Naɗaɗɗun litattafai ɗauke da Litattafan Yahudawa ana karantasu da ƙarfi a cikin majami'unsu.
(Hakanan duba: hatimi, majami'a, maganar Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Irmiya 29:03
- Luka 04:17
- Littafin Lissafi 21:14-15
- Wahayin Yahaya 05:02