582 B
582 B
takalmi, takalma
Ma'ana
Takalmi abin sawa ne a kafa ɗaure da igiya har zuwa ƙwaurinsa. Maza da mata na iya sanya takalmi.
- Akan yi amfani da takalmi a tabbatas da yarjejeniya, kamar sayar da kaya: mutum ɗaya zai tuɓe takalminsa ya bayar ga ɗayan.
- Ta wurin kwaɓe takalmi alama ce ta bangirma, musamman a gaban Allah.
- Yahaya yace bai cancanta ya kwance takalman Yesu ba, wanda shi ne aikin bara marar daraja ko bawa.
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 07:33
- Maimaitawar Shari'a 25:10
- Yahaya 01:27
- Yoshuwa 05:15
- Markus 06:7-9